KARSHEN LUWADI MUGUN
ABOKI MABUDIN WAHALA
PART 2
"Kasan shaheed bashi da lafiya
yau kusan kwana Tara" wallahi
bani da Labari sai yanzu daka fadamin Allah Sarki mai ya sa
meshi
"Abin sai ahankali yan zuma haka
yana asubitin (zana)" bansan
lokacin danai saurin firgitaba!!!
Nagyara zama nace shaheed yana asubitin zana ?
"Wallahi yana can yakamata gobe
muje muduba shi" bansan
lokacin da gumi ya ketomin ba
nace Allah ya kaimu darai da
lafiya mukai sallama na ajiye wayar
Ba,abinda ya fara fadomin acikin
zuciya sai maga nar da
Lawan yacemin gobe zamuje
asubitin zana
Kai da ga jin sunanshi yayi kama da sunan laya wacce ake
cewa layar bata layar zana kodai
shima yayi layar zanar ne ?
Bantaba zuwa asubitin ba amma
duk naji abinda yake faruwa
acikin asubitin Asubitin bangare bangare ne a
yanda na samu Labari akwai
bangaran masu cutarnan ta masu
tari akwai bangaran masu
cutarnan ta zamani mai karya
garkuwar jiki wacce akafi Sani da HIV Ba,abinda zuciyata take
kara sanarmini illah gobe
zakaje asubitin zana bansan
lokacin da hawaye suka fara zubo
minba naidai zuciya ta taci gaba da
mirgino min manya manyan maganganu gobe zakaje
asubitin zana wai shin inkaje
awanne bangare zakaje ?
Bangaren yan tari muci gaba da
karbar magani kafin sa,i yayi ko
kuma bangaran gawa dare zakaje ?
In har bangaran Yan tari zakaje to
yaushe shaheed yafara tari
bamu Sani ba ?
In kuma bangaran gawa darai
zamuje ainaga shaheed baya neme neman mata balle in ce koya
fada rijiya mai gaba dubu
wacce tsalle daya ake afada
cikinta amma sai kai dubu baka
fito ba nan zuciyata taci gaba da
sani cikin halin damuwa da tunani da tausaya wa bansan
lokacin da bacci yai awan gaba
daniba Sai jinai ana bubbuga
kyauran kofar shagona ba sai jinai
ana cewa "mai kakeyi har anfito
daga sallar asuba" Bansan lokacin danai saurin tashi
ba nabude kofa na dau buta
naje nayi alwala nadawo nayi
sallah jinai zuciyata tana cewa
gaskiya yau kayi asara ga shi
bakasamu sallar asuba ba gashi anjima zakaje asubitin zana nan
nafara zare ido
Damisalin karfe sha daya na safe
na dauki wayata nakira
Lawan muka gaisa yace min
"dama yanzu nake shirin inkiraka sai ga kiranka ya shigo dafatan
kashirya ko yanzu ma haka ina
bakin titin layinmu zan hau abin
hawa sai nazo muwuce amma
kafito bakin titi yanda innazo sai
mu wuce, ok karka damu munti kadan sai gamu alayi su
Lawan muka tsaya ya shigo
muka tafi muka nufi asubitin (zana)
Muna tafiya gabana yana faduwa
Lawan yanamin magana
amma zuciyata bata bari na,iya sauraron maganar da Lawan
yakeyimin ba nikon cewa nake eh
bamu jima muna tafiya ba
sai gamu abakin asubin (zana)
muka sallami mai abin hawa
muka tsallaka muka sayi kayan dubiya Wanda a al,ada baya
wuce dan lemo muka siya muka
wuce kai tsaye acikin asubitin
Wednesday, May 15, 2019
Home
Unlabelled
KARSSHEN LUWADI MUGUN ABOKI PART 2
KARSSHEN LUWADI MUGUN ABOKI PART 2
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa

No comments:
Post a Comment