ROMON DIMOKRADIYYA
Kabiru Yusuf Fagge
Gajeren Labari
Muna tafe, tafiya mai nisa, kuma mai wahala, duk
da motar da muke ciki akwai na'urar sanyaya
wuri da kuma tausasan kujeru da nutsuwa, amma
a hakan duk na jigata saboda rashin kyan hanya
ga kuma zafin rana.
Cikin damuwa, na dubi Cif Kamfen na ce masa,
"Wai shi ma wannan garin da za mu je, duk a
cikin jihar Natsira yake?"
Cif Kamfen ya yi dariyar yake, shi ma dai kallona
yake yi, ya ce "Honorabil ka manta ne, wancan
karon fes tenuwa ai mun zo, garin Kumaji ne fa,
ka tuna da muka zo, har muka yi musu
alkawaruka, wadanda sun fi damuwa da batun
ruwan sha..."
Na yi shiru ina tunani, can dai na tuna din,
"Gaskiya kam, sai yanzu na tuna, ni tuni ma na
manta da su da dukkan alkawuran da muka yi
musu a wancan lokacin kafin mu ci zabe..."
"Kuma ka ga kamar yadda ka ce ka manta da
garin, haka ma mun manta ba mu cika musu
alkawarukan da muka daukar musu ba." Cewar
Cif Kamfen.
Na girgiza kai, "Kwarai kuwa, ai abin ne da yawa,
gari kamar Natsira ba karamin gari ba."
Cif Kamfen ya dube ni, "To yanzu dai ga shi mun
dawo gare su da wata bukatar ya kake ganin za
a yi?"
Na yi murmushi, "Idan ka dubi wahalar tafiyar
nan da hanyar nan, ka san da wuya a samu masu
ilimi a garin nan, bare kuma wayayyu, kawai
muna zuwa zan sake yi musu wani alkawarin,
don su sake zabarmu, daga baya idan mun tuna
da su sai mu yi musu rijiyoyin burtsatse ko guda
biyu ne, idan kuma mun manta shi kenan, ai ba
su kadai ba ne mutanen jihar nan ba." Na
kammala maganar tawa ina wage baki cikin
yake, a raina Allah-Allah nake mu je garin mu yi
abin da zamu yi, mu baro su.
Na lura da irin kallon da Cif Kamfen yake yi min,
a zahiri yana so ya gaya min abin da na fada ba
daidai ba ne, amma kawai ya yi min shiru. Kuma
ni da shi mun san abin da muke yi zalunci ne,
amma mun take gaskiya.
Lokacin da muka karasa cikin garin Kumaji, a
raina na tabbatar lallai garin ya ci sunansa
kumaji, gabadaya a cikin damuwa nake, farinciki
daya da ya darsu a raina, shi ne da muka tarar
da mutanen garin suna jiranmu. Na dubi Cif
Kamfen na ce, "Wai har kun cika aiki, kun tara
mutane?"
Cif Kamfen ya ce "Kwarai kuwa, ai tun kwanaki
hudu da suka wuce na sa aka gaya wa Dagaci
zuwanmu, kuma ka san ba zai ki tara wa
maigirma Gwamna mutane ba. Idan ka lura ma,
da alamu tun dazu suke jiranmu."
Na ce, "Na ga alama, to mu yi sauri, mu gama
abin da ya kawo mu, mu bar kauyen nan, wallahi
na gaji."
Babu bata lokaci muka firfito daga cikin
motocinmu, muka hau kan dandamalin da aka
tanadar mana don yi wa jama'ar bayanin
makasudin zuwanmu, da kuma bukatar kuri'unsu.
Sai dai na lura da al'ummar garin, ba kamar na
sauran garuruwan da muka jejje ba, wadanda
suke rinka yi mana kirari da bambadanci, su
wadannan sun yi jugum, suna ta muzurai kamar
mayu. Koda yake ba lallai ba ne su gane fifikon
matsayina na gwamna ba, don haka na yi musu
uzuri.
Shugaban jam'iyya ne ya fara jawabi, sannan ya
gabatar da ni a matsayin gwamnan jiha, kana ya
nemi jin wani abu daga bakin Dagaci.
Dagacin garin, wani tsoho ne wanda ya haura
shekaru tamanin a raye, yana dogara sanda ya
matso kusa damu, a tare da shi akwai wani
saurayi dauke da ruwa a cikin wata
matsakaiciyar kwarya, ruwan ya yi fari-farin farar
kasar . Haka muka tsaya muna kallonsu cikin
mamaki, tare da tunanin ko dai mutanen nan
wani siddabaru za su yi mana na cin zabe, don
mu komai ma muna maraba da shi in dai yadda
zamu ci zabe ne.
Dagaci ya fara magana cikin rawar murya ya ce,
"Maigirma gwamnanmu, a wancan zuwan kafin
ka hau wannan kujera, lokacin da ka zo neman
mu zabe ka, ka yi mana alkawarin samar mana
da tsaftataccen ruwan da zamu rinka sha muna
ibada, da amfanin yau da kullum, to wannan shi
ne ruwan da muke yin duk wadancan abubuwan
da su..." Dagaci ya nuna kwaryar ruwan nan,
"Al'ummar wannan kauye sun ce sun yarda za su
zabe ka, amma a matsayinka na bako sai ka sha
wannan ruwan, wanda yanzun nan aka debo shi
daga gulbi saboda girmama bakinmu."
Dagaci ya umarci saurayin nan ya miko mana
ruwan, ni da Cif Kamfen muka yi wa juna kallon-
kallo, cikin karfin hali na mika hannu na karbi
kwaryar don in nuna musu zan sha. Abin da ba
su sani ba, a irin wannan lokacin babu abin da ba
zan iya yi ba, don samun kuri'arsu. Na karba.
Ina kai kwaryar saitin bakina tare da kokarin
runtse idona don kar in ga yadda ruwan yake,
don in samu in sha a haka, amma sai wani wari
mafi gigitawa ya daki hancina, na yi yunkurin
cillar da kwaryar, amma na sai na fasa, haka dai
na yi jim na 'yan sakanni kaina na juyawa, ban
san lokacin da na kifa kai, na kurbi ruwan ba,
wanda har wani galmi-galmi yake yi, kamar
wanda aka jika karkashi a cikinsa.
Amai ya antayo zai fito min na guntse shi, na yi
kicin-kicin, na mayar da shi, idanuna suka yi
gulu-gulu don ma a cikin gilas suke. A haka, cikin
wannan halin aka ba ni dama, na samu, na dan
furta 'yan kalmomin da kowa a wurin ya san ba a
nutse nake ba, ni kaina ban san abubuwan da na
fada ba, na san dai kalamai ne na karya da
alkawura da muka saba wadanda na dade da
haddace su, muka yi abin da ya kawo mu, muka
bar kauyen nan.
Tun da muka bar kauyen Kumaji na shiga halin
rashin lafiya, don haka babu wani waje da muka
kara zuwa, sai gida. A haka na kwana cikin
rashin lafiya, washegari ma na farka ba lafiya,
ban yi wata-wata ba, na sa aka shirya tafiya ta
zuwa Jamus, don a duba lafiyata kar in mutu a
banza, ban koma kan kujerata ba.
Sai dai abin da ban sani ba, 'yan jarida da 'yan
midiya sun fahimci duk abubuwan da suka faru,
don haka wasu daga cikinsu wadanda ba ma
toshewa baki da cin hanci, da wadanda ba su
yarda da cin hanci ba, suka rubuta labari a kan
hakan, suka watsa.
Wannan shi ya hana ni zarcewa a kan kujerata,
na yi biyu babu, ga rashin lafiya, ga rasa kujera.
Sai dai akwai tunanin da ya fi damuna, shi ne; su
al'ummar Kumaji irin wannan ruwan suke sha
kuma su rayu? Wa zai ba ni amsa?
Na gode.
Kabiru Yusuf Fagge
Thursday, May 16, 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa

No comments:
Post a Comment