KARSHEN LUWADI MUGUN
ABOKI MABUDIN WAHALA
Part 3
@na Faisal Ahmad
07050222260
Da shigarmu cikin a subitin naga lawan ya karya kwana yayi
wani bangare Ni kuma ina biye da
shi ragon azancin da nai
shine ban tambaye shi wanne
bangare zamuje kawai sai naga
mun karkata munbi Wata hanya Ina daga kaina akofar da zamu
shiga sai naga anyi wani rubutu an
rubuta kamar haka alamar
gurin da zamu shiga gurine
namasu dauke da cutar HIV nan
gabana yafadi na kama sallar lami da sauri nace Lawan bakaga
in da zamu shiga bane Lawan
yace "ai anan bangaran suke"
zuciyata taso tabijiromin da
sababbin tunani sai nai ajiyar
numfashi nace nan bawajan tunani bane nan wajan dubiya ne
da daukar darasi
Lawan yana tafe ina binsa abaya
muka tsaya a bakin wani daki
kofa ce amma da kadubi yanayin
kofar bawai daki bane irin shago Mai gado daya da sauran
tarkace
Shigarmu keda wuya cikin dakin
sai idona ya kaini ga hangen
farkon dakin da kar shen dakin
babban daki ne dogo yana dauke da wasu fararan ga daje irin
dai na sauran asubutocin
Muka karasa chan karshen dakin
Wanda a nan ne aka kwantar
da su shaheed ganin Safiyya a kar
shen dakin shiya kara tabbatar min shaheed shine a cikin
wannan dakin
Safiyya kan wace ga shaheed
wanda shekarunta basu wuce
goma sha takwas ba
Kyakykyawa ce ta gaske ta buga musali domin idan akace ma
ana gasar Nuna cikokkun
kyawawan mata nagani nafada
bazaka taba shayin dauko ta
kanunata a cikin dubun dubatar
taron nuna kyawawa mata ba a don ta kawai kansa Yan mata
su buya yayin da take do so wa
Safiyya fulani ne gaba da baya
gaskiya Allah yayi musu kira ta
gaban musali dukan su matan da
mazan Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa Ma haifiyar su
mutuniyar kirki ce ta bugawa
ajarida
Bansan lokacin nadawo daga halin
da zuciyata tajefani ciki ba
tunanin da bai da amfani a irin wannan wajan
Jinai wata zazzakar murya cikin
tausayawat "ina kwananku"
Safiyya ce take gaishemu muka
amsa muka ce ya mai jiki tace
"da sauki" nace mata ina mama "yanzu tafita tace zatadawo"
muka zauna agefan gado
Idanunsa abude muka gaisa yana
magana yana kuka nayi
mamakin yanda naga shaheed ya
rame yayi wani irin bushewa Da yake tunda muka taho zuciyata
ta fara tafiya yawo amma a
wannan karon na hanata zuwa ko
ina Lawan ya dubi Safiyya
wadda kanta yana kasa tun bayan
da muka gaisa "Safiyya Ko zaki tafi gida kihuta tunda munzo
kinga zamu kai har yamma
anan" Safiyya ta dauko filas din
shayi "to natafi"
Muka juyo da hankalin mu kan
shaheed ya saukin jiki akaro na biyu har yanzu yana kallon mu
yana zudda hawaye Mukan sai
rarrashin sa muke kayi hakuri
shaheed kaddara ce tana kan
kowa haka Allah ya kaddara sai
dai kayi hakuri karike ta haka rayuwar duniya dama take cikin ta
akwai kura kurai sai Wanda
Allah ya tserar bu dar bakin
shaheed sai jinai yace "Lawan Ku
Allah ya tserar daku daga
fituntunun duniya dasan abin (Kawa)
Danu na isa da rashin ta wakkali
da abinda Allah ya baka da
rashin godiyar allah"
"Lawan yace shaheed Kana irin
wannan maganar kowa fa da irin kaddarar sa"
"Shaheed yace to ni wannan itace
kaddara ta Wanda ko ban
fada muku ba kunsan halin dana
ke ciki a halin yanzu Wanda
San duniya ne ya jefani cikin irin wannan mugun bakin halin
Dana ke ciki ga shi zan je na hadu
da allah mahaliccina in je in
ce mai me ?
nace kayi hakuri ka dai na kuka
shaheed Allah zai baka lafiya "mai waka wannan cutar bata tashi
ba ce Allah ka tsine wa
Dauda badu !! Lawan kada ku
sake kui irin rayuwar da na tsinci
kai na a ciki mummunar rayuwa
wacce nayi asara acikin ta karshe na ladama da jin kunya zan
bar abin fade ga iyayena da
dangina da ku kanku abokaina zan
bar muku abin zargi da kin
amin cewa daku acikin dubban
jama,a ina son kuyi hakuri da abinda na jefaku a cikin garari
kuya femin abinda nai muku ko
ban fada ba kunsan abinda yake
da muna amma bakusan
mussababin abinda ya jamin ba
Allah ya tsine wa Dauda badu ! Wanda shiyai sanadiyar samin
wannan cutar mai waka ina
kara fada muku kada kusake kubi
rudanin zuciyar Ku kui hakuri
kurun gumin kaddara da abinda
Allah ya hore muku na rayuwa Kune abokai nagari na hakika
amma nai wa tsi daku saboda
baku can za goma balle sha biyar
nafada hannun MUGUN
ABOKI MABUDIN WAHALA"
Lawan cikin tambaya Shaheed amma ba,a wajan baby ka dauki
wannan cutar ba?? " awaja
Dauda badu na dauki wannan
cutar" shaheed cikin kauda kai
ya ci gaba da magana Wata rana.
Ina zaune akofar Gida Dauda badu ya zo ya same ni "shaheed
zoka rakani " nace mashi ina
zan rakaka yace dani gidan abinci
zan na cikin G.R.A zan raka
shi amma saiji nai yace yanzu
zamu dawo zamu sami alkairi so sai kai ma zan baka kasan ka
na amsa mai cikin tambaya
amma da wuri zamu dawo ko ??
Wednesday, May 15, 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa

No comments:
Post a Comment